Ma’aikatar Hajji da Ummara ta ƙasar Saudiyya ta baiwa alhazan da za su yi aikin Hajjin bana da kada su fita waje daga ƙarfe 10 na safe zuwa 4 na yamma a yayin zaman Masha’ir, wato kwanaki huɗu da mahajjata ke yi q garin Minna don gudanar da ibadar Hajji.
Haka zalika Ma’aikatar ta gargaɗi mahajjata da kada ma su je Jabal Noor, wanda aka fi sani da dutsen Arfa, a wani mataki na kare alhazai daga tsananin zafi da ake fama da shi a kasar.
Ma’aikatar, ta ce yayin da yanayin zafi ya haura matakin digiri 50⁰c, mahajjata su tabbata sun tafi Muzdalifa daga Arfa a mota saboda kariyar lafiyar su.
Haka zalika ma’aikatar ta sanar da cewa jifan shaidan ma ya kasance rukuni-rukuni don gujewa turmutsutsu da cunkoso.
Sannan ma’aikatar ta yi kira ga alhazai da su kai rahoton duk wani bako da ya zo tantin su da ba su yadda da shi ba.