Alhazan farko na Katsina sun sauka Makkah

by admin

Alhazan farko na jihar Katsina su 566 sun kammala kwanakin su ma Madina sun kuma isa birnin Makkah.

Maniyatan, wadanda suka fito daga shiyyoyin Mani da Malumfashi sun sauka Birnin Makkah afiya da walawala, inda tuni aka sama musu masauki.

A cewar kakakin hukumar alhazai ta jihar, tuni sun kammala dawafin su na Ummara a jihar da daddare.

A wani sashen kuma, Kwamitin Misha,’ir na Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Katsina a yau sun fara ziyar tar Minna da Arafat domin tabbatar da komai na gudana lafiya.

Sakataren Kwamitin, Alh.Badaru Bello Karofi,  madadin Shugaban Kwamitin, Mallam Nasir Ahmed ne ya wakilci sauran ƴan kwamitin domin dubawa da karbar yankuna da kuma sauran kayayyakin hidima ga maniyyatan a nan Minna da kuma Arafat.

You may also like