Hajji 2026: Saudiyya Ta Bayyana Jadawalin Jigilar Mahajjata

by admin

 

 

Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Saudiyya (GACA) ta fitar da jadawalin yadda tsarin zirga-zirgar jirage za ta kasance yayin Hajjin 2026/1447.

 

Kamar yadda jadawalin ya nuna, jigilar rukunin farko na maniyyata za ta kankama ne a watan Afrilu 8, 2026 (1/11/1447 AH), sannan a kammala a ranar Alhamis, 21 ga Mayu, 2026 (4/12/1447 AH), bisa lisaffin kalandar Umm Al-Qura.

 

Sannan jagilar alhazai zuwa gida bayan kammala aikin Hajji, za ta kankama daga ranar Asabar, 30 ga Mayu, 2026 (13/12/1447 AH), a kammala a ranar Talata, 30 ga Yuni, 2026 (15/01/1448 AH).

 

GACA ta jaddada cewa, dole a gabatar da dukkan buƙatun jirage tsakanin ranar Lahadi, 29 ga Agusta, 2025 (01/03/1447 AH), da ranar Alhamis, 12 ga Maris, 2026 (23/09/1447 AH). Hukumar ta kuma buƙaci a kammala yarjejeniyoyi da hukumomin Hajji a kan jari domin tabbatar da sauƙin masauki da shirye-shiryen sufuri a Makka da Madinah.

 

Ta ƙara da cewa, yayin da ya zamana an samu saɓani tsakanin kalandar Hijira da ta Miladiyya, za a yi amfani da kalandar Miladiyya wajen gudanar da zirga-zirgar jiragen.

 

Daga nan, Hukumar ta yi gargaɗin ɗaukar matakin doka kan duk wani kamfanin jirgin saman da ya saɓa ƙa’idojin sufurin da aka gindaya.

You may also like